logo

HAUSA

IOM: Sama da bakin haure 75 sun nitse a tekun Libya

2021-11-21 16:52:30 CRI

Hukumar kula da makaurata ta kasa da kasa (IOM), ta bayyana a ranar Asabar cewa, sama da bakin haure 75 sun nitse a gabar tekun yammacin kasar Libya, a yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai.

A sakon da ta wallafa a shafin twita, IOM ta ce, sama da bakin haure 75 sun nitse a ranar Laraba bayan sun tashi daga Libya, kamar yadda wasu mutane 15 da suka tsira bayan da masu kamun kifi suka kubutar da su suka fada, inda suka mayar da su zuwa yankin Zuwara.

A cewar IOM, hadarin na baya bayan nan ya sanya adadin hasarar rayukan da aka samu a tsakiyar tekun Mediterranean a wannan shekarar ya kai sama da mutane 1,300.

Kasar Libya ta jima tana fama da matsalolin tabarbarewar tsaro da rikice-rikice tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi, a shekarar 2011, lamarin da ya mayar da kasar ta arewacin Afrika tamkar wata babban matattarar kwararar bakin haure ta barauniyar hanya dake neman tsallaka tekun Mediterranea don zuwa kasashen Turai.(Ahmad)