logo

HAUSA

Yawan Makamashi Mai Tsafta Na Kasar Sin Ya Karu Tsakanin Janairu Zuwa Oktoban Bana

2021-11-20 15:32:38 CMG

Yawan Makamashi Mai Tsafta Na Kasar Sin Ya Karu Tsakanin Janairu Zuwa Oktoban Bana_fororder_1120-energy-Faeza

Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin, ta ce yawan makamashi mai tsafta da kasar Sin ke samarwa ya karu sosai cikin watanni 10 na farkon bana.

A cewar hukumar, zuwa karshen watan Oktoba, jimilar makamashi da tashoshin da kasar Sin ta kafa ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 2.3, wanda ya karu da kaso 9 a kan na bara.

Yawan makamashin da ake samarwa daga karfin iska ya karu da kaso 30.4 a kan na bara, zuwa kilowatt miliyan 300, yayin da wanda ake samu daga hasken rana, ya tsaya kan kilowatt miliyan 280, adadin da ya karu da kaso 23.7.

Kasar Sin na samun ci gaba a fannin habaka makamashi mai tsafta yayin da take kokarin rage hayaki mai dumama yanayi.

Kasar ta sanar da cewa, za ta yi kokarin kai wa matsayin koli na fitar da sinadarin Carbon a shekarar 2030, sannan ta cimma burinta na daidaita yawan sinadarin da abubuwan dake shanyesu a shekarar 2060. (Fa’iza Mustapha)

Faeza