logo

HAUSA

Sashen CCTV-16 ya kaddamar da shirin nuna ruhin Olympics da kayayyakin fasaha

2021-11-20 15:55:22 CRI

Sashen CCTV-16 ya kaddamar da shirin nuna ruhin Olympics da kayayyakin fasaha_fororder_CMG

Sashen watsa wasannin Olympics na CCTV wato CCTV-16 na babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin wato CMG, ya kaddamar da sabon shirin nuna ruhin wasannin Olympics da kayayyakin fasaha a hukumance, inda shugaba kuma babban editan CMG Shen Haixiong ya halarci bikin kaddamar da shirin.

An tsara sabon shirin ne domin nuna al’adu da ruhin Olympics ta hanyar bayani kan kayayyakin fasaha.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin kaddamar da shirin, shugaban CMG Shen Haixiong ya jaddada cewa, babban sakataren JKS Xi Jinping ya yi nuni da cewa, ya dace sashen CCTV-16 ya mai da hankali kan aikin yada labarai da ruhin wasannin motsa jiki na kasar Sin ta hanyar yada al’adun wasannin Oluympics, haka kuma ya ingiza cudanyar wayewar kan kasashe daban daban a fadin duniya ta hanyar kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren wasannin motsa jiki.(Jamila)