logo

HAUSA

An ceto ‘yan ci rani 302 gabar ruwan Libya

2021-11-20 15:31:10 CMG

An ceto ‘yan ci rani 302 gabar ruwan Libya_fororder_1120-Libya-Faeza

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta ce jimilar ‘yan ci rani 302 aka ceto daga teku, inda aka mayar da su Libya.

Hukumar ta wallafa a shafin tweeter cewa, an ceto ko kama mutane 302 daga teku a daren Alhamis yayin wasu ayyuka 3 da ta gudanar, inda aka kai su Tripoli da Zawiya.

Ta ce daga cikinsu, akwai mata 50 da yara 22, tana mai cewa hukumar da kungiyar agaji ta Red Cross sun samar musu da kulawar lafiya da kuma kayayyakin bukata.

Libya na fama da matsalar tsaro da tashin hankali tun bayan rushewar mulkin Muammar Gaddafi a shekarar 2011, lamarin da ya sa kasar ta zama hanyar da ‘yan ci rani ke bi don tsallake tekun Bahar Rum zuwa Turai.

Yawancin wadanda ake cetowa daga teku na karewa ne a cibiyoyin da ake tsugunar da ‘yan ci rani a Libya, wadanda ke cike da jama’a, duk kuwa da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na a rufe irin wadannan cibiyoyi. (Fa’iza Mustapha)

Faeza