logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon taya murna ga taron wayewar kai a fannin intanet na farko na kasar

2021-11-19 14:45:44 CRI

Xi ya aike da sakon taya murna ga taron wayewar kai a fannin intanet na farko na kasar_fororder_211119-Faeza 2

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taro karon farko na kasar, kan wayewar kai a fannin intanet, wanda aka bude a yau Juma’a.

Cikin wasikar tasa, Xi Jinping ya yi kira da a hada hannu, tare da kara kai mai da kyautawa juna wajen kyautata amfani da kafar intanet.

Ya ce a matsayin muhimmin bangaren na harkokin al’umma da waye a sabon yanayi, wayewar kai a fannin intanet na da muhimmanci wajen inganta karfin kasar Sin a wannan bangare.

Da yake jadadda muhimmancin ciyar da bangaren gaba da kuma tafiyar da shi yadda ya kamata, shugaba Xi ya bukaci dandamalin intanet da kungiyoyin al’umma da masu amfani da kafar intanet, su taka muhimmiyar rawa wajen inganta wayewar kai a fannin intanet. (Fa’iza Mustapha)