logo

HAUSA

Putin ya yi tsokaci kan dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin

2021-11-19 19:16:51 CRI

A yayin da yake mayar da martani ga kyawawan furucin da shugaban kasar Rasha Putin ya yi kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa Jumma’ar nan cewa, wannan ya nuna matukar muhimmanci da kasar Rasha, musamman ma shi kansa shugaba Putin ke baiwa ci gaban dangantakar Rasha da kasar Sin. Kasashen biyu su ne fifikon diflomasiyyar juna. Kasashen Sin da Rasha abokan hadin gwiwa ne na gaskiya, wadanda ba za a iya rabawa ko murkushe su ba.(Ibrahim)