logo

HAUSA

Sin za ta mayar da hankali kan bangarori uku domin inganta ci gaban masana'antu na karkara

2021-11-18 20:26:57 CRI

Sin za ta mayar da hankali kan bangarori uku domin inganta ci gaban masana'antu na karkara_fororder_noma

Ma'aikatar noma da raya karkara ta kasar Sin ta sanar a yau cewa, domin ganin an habaka masana'antun karkara, kwanan baya ma'aikatar ta fitar da wani kundi dake zama jagora, wanda ya bayyana karara kan yadda za a mayar da hankali kan manyan ayyuka guda uku, da nufin inganta masana'antun karkara.

Na farko shi ne fadadawa da karfafa masana’antun sarrafa kayayyakin amfanin gona. Na biyu shi ne inganta sashen yawon shakatawa na karkara da zama mai amfani. Na uku, yin aiki tukuru don zama sabon kasuwancin intanet na karkara.(Ibrahim)