logo

HAUSA

Sin ta shirya shigar da kudade cikin ayyukan kyautata amfani da kwal

2021-11-18 11:13:03 CRI

Sin ta shirya shigar da kudade cikin ayyukan kyautata amfani da kwal_fororder_s02-China to introduce targeted re

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce Sin za ta zuba kudade masu tarin yawa, a aikin kyautata amfani da makamashin kwal, da nufin tallafawa manufar rage fitar da nau’o’in iskar Carbon mai dumama yanayi. Firaministan ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin zaman majalissar gudanarwar kasar Sin da ya jagoranta.

Li Keqiang ya ce, duba da yadda kasar Sin ke cin gajiya daga makamashin kwal, yana da muhimmanci a yi la’akari da ainihin halin da kasar ke ciki, a yi aiki tukuru wajen tsaftace hanyoyin amfani da kwal bisa dabaru mafiya inganci.

Ya ce "A halin da ake ciki, kwal na cikin makamashi da kasarmu ke dogaro da shi. Hakan kuma zai dore zuwa wani lokaci mai tsawo, lamarin dake da nasaba kwarai da ci gaban kasarmu. Don haka akwai bukatar mu aiwatar da sauye-sauye a kan hanyar mu ta ci gaba. Ma’ana dai, ba za mu iya tsayawa kan tafarkin ci gaba mai tattare da tsananta amfani da makamashi ba"

Daga nan sai firaminista Li ya bayyana shirin gwamnatin Sin, na samar da kudade har kimamin dalar Amurka biliyan 31.3, wadanda za a yi amfani da su wajen aiwatar da fasahohin bunkasa kasa tare da rage fitar da iskar Carbon, baya ga sauran kudaden da kasar ta ware a baya na aiwatar da wannan manufa.  (Saminu)