logo

HAUSA

Ya dace Sin da Congo su karfafa hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin su in ji firaminista Anatole Makosso

2021-11-17 10:33:12 CRI

Ya dace Sin da Congo su karfafa hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin su in ji firaminista Anatole Makosso_fororder_211117-Saminu1-Congo

A jiya Talata ne firaministan janhuriyar Congo Anatole Collinet Makosso, ya bayyana fatan ci gaba da inganta hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin Sin da Congo.

Firaminista Makosso ya bayyana hakan ne, cikin jawabin sa na bude dandali karo na 4, na hadin gwiwar kananan hukumomin Sin da na kasashen nahiyar Afirka wanda ya gudana ta kafar bidiyo. Taron ya hallara manyan jami’an jam’iyyun siyasa kusan 300 daga kasashen Afirka daban daban, da jami’an gwamnatocin kananan hukumomi, da cibiyoyi masu ruwa da tsaki daga sassan biyu.

Kaza lika firaministan na Congo, wanda ya gabatar da jawabinsa daga birnin Brazzaville, ya jinjinawa mahalarta taron, wanda ya haskakawa duniya irin kyakkayawar dangantaka da kusanci dake tsakanin sassan biyu.

Makosso ya ce gwamnatin Congo, na dora muhimmanci ga ci gaba da bunkasa hadin gwiwa tsakanin kananan hukumomin sassan biyu, inda ya yi bitar wasu daga kyawawan sakamako da hakan ya haifar ga sassan biyu.

Bugu da kari, firaministan na Congo, ya zayyana alakar biranen sassan biyu, da tallafin kayan kiwon lafiya na yaki da cutar COVID-19 da biranen Sin suka samarwa kasar Congo, da ma ziyarar da jami’an kasashen biyu ke kaiwa juna, a matsayin fa’ida dake kara karfafa hadin gwiwar kananan hukumomin Sin da na Congo.   (Saminu)