logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi alkawarin fadada bude kofa ga waje

2021-11-17 21:39:18 CRI

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta fadada bude kofa ga kasashen waje ba tare da wata tangarda ba, da samar da yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa bisa doka, da kuma mizanin kasa da kasa.

Li ya bayyana haka ne a yayin da yake halartar wata tattaunawa ta musamman da shugabannin 'yan kasuwa na duniya, da taron dandalin tattalin arzikin duniya ya shirya a jiya Talata. Kimanin ‘yan kasuwa 400 daga kasashe sama da 40 ne suka halarci taron. (Ibrahim)