logo

HAUSA

AU ta yi tir da tagwayen hare-haren da aka kai Uganda

2021-11-17 11:15:07 CRI

AU ta yi tir da tagwayen hare-haren da aka kai Uganda_fororder_211117-AU-Fa'iza

Tarayyar Afrika AU, ta yi tir da tagwayen hare-haren da aka kai Kampala, babban birnin Uganda, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 6, ciki har da ’yan kunar bakin wake 3.

AU ta wallafa a shafin tweeter cewa, tana tare da al’ummar Uganda biyo bayan wadannan hare-haren ta’addanci da aka kai shingayen binciken ’yan sanda, a kuma titin dake dauke da ofisoshin gwamnati.

Cikin sakon da ya wallafa a shafin tweeter, shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da hare-haren. Yana mai cewa kungiyar na jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya.

’Yan sanda sun ce mutane 33 sun raunana yayin harin. A cewarsu, hare-haren na da alamu irin na kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) wadda ke mubaya’a ga kungiyar IS, reshen tsakiyar Afrika.

Hare-haren na zuwa ne kimanin makonni 3, bayan wasu hare-hare daban-daban guda biyu, sun yi sanadin mutuwar mutane biyu da raunata wasu da dama, a yankin tsakiyar Uganda. An dora alhakin hare-haren kan kungiyar ADF. (Fa’iza Mustapha)