logo

HAUSA

Amurka na takurawa musulmi da sunan yaki da ta'addanci

2021-11-17 19:15:56 CRI

Amurka na takurawa musulmi da sunan yaki da ta'addanci_fororder_新疆-9

A yau Laraba ne, aka gudanar da taron manema labaru karo na 60 kan batutuwan da suka shafi jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin a nan birnin Beijing. Mai magana da gwamnatin jama'ar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, Xu Guixiang, ya yi nuni da cewa, bisa la'akari da sakamakon yaki da ta'addanci, da kawar da tsattsauran ra'ayi da ake gudanarwa a jihar Xinjiang bisa doka, da kare hakkin bil'adama, wanda ya haifar da zaman lafiyar jama'a da rayuwa da kuma aiki cikin zaman lafiya. Amma Amurka tana keta hakkin dan adam bisa fakewa da "yaki da ta'addanci".

Madam Mailihaba Olan, farfesa a jami'ar Xinjiang, ta kara da cewa, Amurka na nuna wariya ga musulmi da sunan yaki da ta'addanci. A shekara ta 2017, Amurka ta fitar da wani umarni na shugaba mai suna "shirin kariya na kasa don hana 'yan ta'addan waje shiga Amurka", inda ta haramtawa 'yan kasashen Iraki, da Siriya, da Iran da sauran kasashe shiga cikin kasar ta Amurka, wadannan kasashe duk kasashe ne dake yawan musulmi. Wannan al'ada ta danganta ta'addanci da wasu takamaiman kasashe, yankuna, da addinai, ya gamu da suka daga al'ummomin duniya.(Ibrahim)