logo

HAUSA

An gudanar da taron dandalin sada zumunta na kasashen Sin da Afirka a Beijing

2021-11-17 19:25:55 CRI

An gudanar da taron dandalin sada zumunta na kasashen Sin da Afirka a Beijing_fororder_wu hongbo

Jiya ne a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, aka gudanar da taron karawa juna sani karo na 6 na dandalin tattaunawar jama'a tsakanin Sin da Afirka, da dandalin sadarwa na kasa da kasa na Sin da Afirka. Mahalarta taron sun tattauna kan yadda ake tafiyar da harkokin diflomasiyya da sadarwa tsakanin kasashen Sin da Afirka, inda suka yi imanin cewa, kokarin kasar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar Afirka, tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar musaya tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu na Sin da Afirka yadda ya kamata

Shugaban kungiyar hulda da jama'a ta kasa da kasa ta kasar Sin, Wu Hongbo ya bayyana a gun taron cewa, dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka, ta fuskanci gwaji na dogon lokaci, kuma tana da tushe mai inganci. (Ibrahim)