logo

HAUSA

Kasar Sin: Ya Zuwa Shekarar 2025 Za A Kafa Tsarin 5G Mafi Girma A Duniya

2021-11-17 13:56:42 CRI

Kasar Sin: Ya Zuwa Shekarar 2025 Za A Kafa Tsarin 5G Mafi Girma A Duniya_fororder_5G

Yanzu yawan tasoshin 5G ya wuce miliyan 1 da dubu 150 a kasar Sin, wanda ya zarce kaso 70 cikin dari bisa jimillar tasoshin a duniya. Kasar Sin ta kafa tsarin 5G mafi girma kuma mafi ci gaban fasaha a duniya. Yawan masu amfani da fasahar 5G ya kai miliyan 450 baki daya a kasar Sin, wanda ya wuce kaso 80 cikin dari bisa jimillar masu amfani da fasahar a duniya.

Bisa abubuwan da aka tanada cikin Shirin raya kasar Sin na shekaru biyar biyar karo na 14 dangane da bunkasa sana’ar aikin sadarwa, kasar Sin za ta yi namijin kokarin kafa tsarin 5G mafi girma ya zuwa shekarar 2025. Xie Cun, shugaban sashen raya aikin sadarwa na ma’aikatar masana’antu da aikin sadarwa ta kasar Sin ya yi karin bayani da cewa, kasar Sin tana namijin kokarin kafa tsarin 5G mafi girma ya zuwa shekarar 2025, tare da ganin akwai tasoshin 5G guda 26 cikin kowadanne mutane dubu 10. Sa’an nan kasar Sin tana kokarin tabbatar da shimfida tsarin 5G a dukkan birane da garuruwa da ma muhimman wurare, inda kuma za a shimfida tsarin a kauyukan da yawansu ya kai kaso 80 cikin dari. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan