logo

HAUSA

Sin ta zama kasa mai karfin tattalin arziki mafi girma da samu karuwar yankin gandun daji

2021-11-17 19:43:08 CRI

Sin ta zama kasa mai karfin tattalin arziki mafi girma da samu karuwar yankin gandun daji_fororder_gandun daji

Hukumar kula da gandun daji da ciyawa ta kasar Sin ta sanar a yau Laraba cewa, daga shekarar 2007 zuwa 2020, yankin gandun dajin da ke yankin Asiya da tekun Pasifik, ya karu da hekta miliyan 27.9, wanda ya zarce burin raya gandun daji na yankin. A matsayinta na mamba a kungiyar APEC, yankin gandun dajin kasar Sin ya karu da hekta miliyan 26.5 a cikin wannan lokaci, wanda ya kai kusan kashi 95 cikin 100.

Sakamakon haka, kasar Sin ta zama kasa mai karfin tattalin arziki da ta samu karuwar gandun daji a tsakanin kasashe 21 na kungiyar APEC. (Ibrahim)