logo

HAUSA

Yawan cinikayya tsakanin Sin da Afrika ya kai dala biliyan 185 cikin farkon watanni 9 na bana

2021-11-17 14:35:22 CRI

Yawan cinikayya tsakanin Sin da Afrika ya kai dala biliyan 185 cikin farkon watanni 9 na bana_fororder_211117-AU-Fa'iza

Yawan cinikayya tsakanin Sin da Afrika ya kai dala biliyan 185 daga watan Junairu zuwa Satumbar bana, wanda ya karu da kaso 38.2 cikin dari a kan na bara, ya kuma kai wani sabon matsayi.

Mataimakin ministan kula da cinikayya na kasar Sin, Qian Keming, ya ce kasar Sin ta kasance mai inganta daidaito a cinikayyarta da Afrika, kuma ba ta taba neman ingiza rarar cinikayya tsakaninta da Afrika ba. Ya ce a shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta yi kokarin kara shigar da kayayyaki daga Afrika ta hanyar wadannan matakai:

Na farko, fadada hanyoyin da kayayyakin Afrika za su shiga kasuwar kasar Sin. Misali, baje kolin cinikayya da tattalin arziki na Sin da Afrika da aka kafa musamman saboda kasashen Afrika, sannan an kafa cibiyar sarrafawa da rarraba kayayyakin Afrika a Changsha na lardin Hunan, wadda ba ta tanadi kayayyakin da ba na albarkatu ba, haka kuma an kafa cibiyar nune-nune da sayar da kayayyakin Afrika a Yiwu na lardin Zhejiang.

Na biyu, ana bukatar saukaka cinikayya tsakanin kasashen Afrika da Sin. Don haka, Sin ta soke haraji kan kaso 97 na kayayyakin da aka shigar da su kasar daga a kalla kasashen Afrika 33.

Na uku, samar da tallafi ga masu fitar da kayayyaki daga kasashen Afrika zuwa Sin. Kasar Sin ta kafa asusu na musamman na dala biliyan 5 domin shigo da kayayyaki daga Afrika da nufin tallafawa kamfanonin Sin din dake shigo da kayayyaki daga Afrika.

Na hudu, ana bukatar Afrika ta inganta karfinta na fitar da kayayyaki. Kasar Sin na karfafawa kamfanoninta gwiwar zuba jari a Afrika a fannonin noma da sarrafa kayayyaki da hidimomi da daukaka darajar masana’antu da kayayyakin da ake fitarwa daga Afrika, domin kara darajar kayayyakin da taimakawa nahiyar a tsarin samar da kayayyakin na duniya ta yadda za ta kara samun ci gaba daga mai samar da kayayyakin da ake sarrafawa zuwa samar da kayayyakin da aka riga aka sarrafa, a wani mataki na fadada daidaito a fanin cinikayya tsakanin Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)