logo

HAUSA

An ba da shawarwarin raya jihar Xinjiang bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”

2021-11-16 11:10:45 CRI

An ba da shawarwarin raya jihar Xinjiang bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”_fororder_微信图片_20211116111024

Jiya Litinin, aka bude taron raya jihar Xinjiang na shekarar 2021 a birnin Beijing. Mahalarta taron sun ba da shawarwari iri-iri domin neman bunkasuwar jihar bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da kuma ba da gudummawar gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa.

Jihar Xinjiang tana tsakiyar nahiyar Asiya da nahiyar Turai, a zamanin da, ta zama muhimmiyar gada dake tsakanin kasar Sin da yammacin kasashe. Yanzu, jihar Xinjiang ta zama muhimmiyar hanyar mu’amala a tsakanin kasashe masu halartar shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kuma, ta kasance muhimmin matakin kasar Sin wajen habaka hadin gwiwa da yammacin duniya, da kuma raya tsarin bude kofa ga waje bisa dukkan fannoni.

Bisa bayanin da aka fidda, cikin farkon rabin shekarar bana, jimillar kayyayakin shige da fice a tsakanin jihar Xinjiang da kasashe masu halartar shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta kai RMB yuan biliyan 56.65, adadin da ya karu da kashi 23.1 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar bara, kuma, ya kai kashi 86 bisa dari cikin dukkanin kayayyakin shige da fice na jihar Xinjiang.

Jakadan kasar Argentina dake kasar Sin Gustavo Sabino Vaca Narvaja, ya taba ziyartar jihar Xinjiang, ya kuma ce yanayin muhalli mai kyau da bunkasuwar aikin gona da kimiyya da fasaha a jihar sun burge shi matuka. A yayin taron, ya ce, shawarar “Ziri daya da hanya daya” tana da muhimmiyar ma’ana ga kasarsa. Yana mai cewa,

“Shawarar “Ziri daya da hanya daya” tana tallafawa kasa da kasa, musamman ma, ga yankunan dake yammacin kasar Sin, kamar jihar Xinjiang, domin shawarar ta kasance Karin matakin da kasar Sin ta dauka wajen raya yammacin kasa, shi ya sa, bunkasuwar jihar Xinjiang, da nasarar da aka cimma wajen kawar da talauci a jihar sun janyo hankulanmu sosai. Ko shakka babu, jihar Xinjiang ta samu gagarumin ci gaba cikin shekarun baya bayan nan, ba kawai a fannin raya ababen more rayuwa ba, har ma da kyautata zaman rayuwar al’umma kamar yadda suke fata. ” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)