logo

HAUSA

Ireland ta baiwa fasinjojin da aka yiwa riga-kafin Sinovac da Sinopharm izinin shiga kasar

2021-11-16 16:01:26 CRI

Ireland ta baiwa fasinjojin da aka yiwa riga-kafin Sinovac da Sinopharm izinin shiga kasar_fororder_211116-Ahmad 3

Rahotanni daga shafin intanet na gwamnatin Ireland da aka wallafa a ranar 14 ga wata ya nuna yadda aka sabunta dokokin zirga-zirga na kasa da kasa dake shafar kasar. Gwamnatin Ireland ta lamincewa fasinjojin da aka baiwa cikakkun riga-kafin kamfanonin Sinovac da Sinopharm na kasar Sin cikin kwanaki 14 izinin shiga kasar idan suna dauke da cikakkiyar shaidar karbar riga-kafin.

A halin yanzu, gwamnatin Ireland ta amince da yin amfani da riga-kafin cutar Covid-19 guda shida, da suka hada da kamfanonin Pfizer, Moderna, Johnson & Johnson da AstraZeneca, sai kuma sabbin da kasar ta kara amincewa da su na kamfanonin Sinovac da Sinopharm. (Ahmad Fagam)