logo

HAUSA

Yan sanda a Nijeriya sun ceto mutane 11 da aka sace a jihar Katsina

2021-11-16 10:40:17 CRI

’Yan sanda a jihar Katsina dake arewacin Nijeriya, sun ceto mutane 11 da aka sace, biyo bayan wasu ayyukan yaki da sace-sacen mutane da suka gudanar a maboyar bata gari dake jihar.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua a jiya, Gambo Isa, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Lahadi, kwanaki 2 bayan ’yan bindiga sun sace su, lokacin da suka kai hari kauyen Sabon Garin Safana na yankin karamar hukumar Safana ta jihar.

Har ila yau, ya ce ’yan sandan sun kuma dakile wani hari da ’yan bindiga suka kai kauyen Gidan Duka na yankin karamar hukumar Kankara ta jihar. Yana mai cewa, an yi musayar wuta tsakaninsu da ’yan sanda, kafin daga bisani su tsere cikin daji. (Fa’iza Mustapha)