logo

HAUSA

An kammala taron tattaunawar shugabannin kasashen Sin da Amurka ta kafar bidiyo

2021-11-16 13:28:56 CRI

An kammala taron tattaunawar shugabannin kasashen Sin da Amurka ta kafar bidiyo_fororder_211116-Ahmad2

Da misalin karfe 12:24 na rana agogon Beijing na yau Talata 16 ga watan Nuwamba, an kammala taron tattaunawa karo na farko tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka ta kafar bidiyo.

Shugaba Xi Jinping ya halarci tattaunawa tare da shugaba Biden a birnin Beijing, da misalin karfe 8:46 na safe agogon Beijing, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da huldar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma sauran batutuwan dake shafar moriyar kasashen biyu.

Tattaunawar ta farko ta kafar bidiyo tsakanin shugabannin kasashen na Sin da Amurka, an rabata zuwa kashi na daya da na biyu, kuma an fara kashi na biyu na tattaunawar ne da misalin karfe 11:06 na safe agogon Beijing. (Ahmad)