logo

HAUSA

An shirya taron musamman na 'yan kasuwan duniya ta kafar bidiyo

2021-11-16 19:10:40 CRI

Yau ne, taron dandalin tattalin arzikin duniya, ya gudanar da taron tattaunawa ta kafar bidiyo na musamman ga 'yan kasuwa a duniya. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya gabatar a taron manema labaru da aka saba gudanarwa a wannan rana cewa, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai gabatar da muhimmin jawabi a gun taron tattaunawa tare da musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi 'yan kasuwa.

Zhao Lijian ya ce, kasashen duniya, musamman kamfanoni na kasa da kasa, suna mai da hankali sosai kan yadda ake raya tattalin arzikin kasar Sin, da kuma yadda ake tafiyar da manufofi, kuma gaba daya, suna fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin.(Ibrahim)