logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gabatar da shawarwarin kyautata dangantakar Sin da Amurka

2021-11-16 11:03:13 CRI

Shugaban kasar Sin ya gabatar da shawarwarin kyautata dangantakar Sin da Amurka_fororder_211116-Saminu 1-Sin da Amurka

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, Sin da Amurka na kan wata gaba mai muhimmanci na ci gaba, yayin da duniya ke fuskantar kalubale da dama. A matsayinsu na kasashe mafiya karfin tattalin arziki, kuma masu kujerar naki a kwamitin sulhu na MDD, akwai bukatar Amurka da Sin su kara tuntubar juna da hadin gwiwa, kana kowacce cikinsu ta tafiyar da harkokinta na cikin gida yadda ya kamata, a lokaci guda kuma, su sauke nauyin dake wuyansu ta fuskar batutuwan da suka shafi duniya, su hada hannu domin tabbatar da burin zaman lafiya da ci gaba a duniya. A cewarsa, wannan buri ne na bai daya na al’ummu da shugabannin kasashen biyu da sauran sassan duniya.

Ya kara da jaddada cewa, ana bukatar kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka domin ci gaban kasashen da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya, ciki har da lalubo ingantattun hanyoyin tunkarar kalubale kamar na sauyin yanayi da annobar COVID-19. Ya ce ya kamata Sin da Amurka su rika mutunta juna tare da gudanar da hulda cikin kwanciyar hankali da hadin gwiwar moriyar juna. Bugu da kari, Xi ya ce a shirye yake ya hada hannu da shugaba Biden wajen cimma matsaya guda tare da daukar matakan inganta dangantakarsu. Ya ce yin hakan zai kyautata muradun jama’ar kasashen biyu da fatan al’ummun duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)