logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin hajojin kasashen Afirka na IATF

2021-11-16 10:18:38 CRI

An bude bikin baje kolin hajojin kasashen Afirka na IATF_fororder_211116-Saminu 1-Durban

A jiya Litinin ne aka bude bikin baje kolin hajojin kasashen Afirka na IATF a birnin Durban na Afirka ta kudu, kuma mahalarta baje kolin sun yi amfani da damar hakan, wajen kira da a bunkasa musayar dabaru don inganta cinikayya tsakanin kasashen dake sassan nahiyar.

Da yake tsokaci cikin jawabinsa na budewa, jagoran taron, kuma tsohon shugaban tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo, ya ja hankalin jagororin Afirka da su ingiza burin da ake da shi na gudanar da cinikayya, da musayar kasuwanci a yayin baje kolin. Ya ce IATF zai samar da wani dandali na tattauna kasuwanci domin al’ummar Afirka, da kuma hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar nan ta kafa yankin ciniki maras shinge na Afirka ko AfCFTA a takaice.

Mr. Obasanjo ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa, game da yiwuwar amfani da baje kolin na wannan karo wajen tattauna hanyoyin warware kalubalen cinikayya a Afirka, ciki har da na ketare kan iyakokin kasashen nahiyar.

A nasa tsokaci kuwa, babban sakataren sakatariyar yarjejeniyar yankin ciniki maras shinge ta Afirka Mr. Wamkele Mene, cewa ya yi AfCFTA na da muhimman burika, ciki har da tsamo sama da al’ummun Afirka miliyan 100 daga matsanancin kangin talauci nan zuwa shekarar 2035, da fadada cinikayya tsakanin al’ummun nahiyar. Mr. Mene ya kuma yi gargadin cewa, idan kasashen Afirka suka ki hada kan su, yarjejeniyar ta AfCFTA ba za ta yi nasara ba.  (Saminu Alhassan)