logo

HAUSA

An kashe a kalla mutane 20 a wani hari a arewacin Burkina Faso

2021-11-15 09:51:53 CRI

A kalla mutane 20 aka hallaka da suka hada da jami’an tsaro 19, a wani harin ta’addanci a ranar Lahadi don yaki da jami’an tsaro na Inata gendarmerie, a lardin Soum dake yankin Sahel, ministan tsaron kasar Burkina Faso, Maxim Kone, ya sanar da hakan ta babban gidan radiyon kasar.

Kone ya bayyana cikin sanarwar da aka baiwa manema labarai cewa, ana cigaba da ayyukan sintiri game da faruwar lamarin. An bukaci al’ummun yankin da su sanya ido kana su bayar da cikakken hadin kai ga jami’an sojoji.

Alkaluman da aka bayyana na mutanen da suka mutu a harin na wucin gadi ne, kana babu wata kungiyar da ta yi ikirarin daukar nauyin harin har zuwa karfe 8 na daren ranar Lahadi.(Ahmad)