logo

HAUSA

Kasar Sin na neman ra’ayin jama’a dangane da daftarin kare bayanan intanet

2021-11-15 10:48:31 CRI

Kasar Sin na neman ra’ayin jama’a dangane da daftarin kare bayanan intanet_fororder_260014674476793907

Hukumar kula da kafar intanet ta kasar Sin, ta gabatar da daftarin dake kunshe da jerin ka’idojin tabbatar da tsaron bayanan intanet, domin neman ra’ayin jama’a.

A cewar daftarin, ya kamata kamfanonin sarrafa bayanai su samar da hanyoyin kai dauki na gaggawa, domin takaita illolin da ka iya aukuwa daga barazanar tsaron bayanai.

Daftarin, ya kuma yi tanadin haramta daukar bayanai ta na’ura, kamar na fuska da hoton yatsa, a matsayin hanyoyin shaida mutum, a wani yunkuri na dakile karbar irin wadannan bayanai bisa tilas.

Bugu da kari, daftarin ya ce bai kamata kamfanonin sarrafa bayanai su ki samar da hidimomi ko su kawo tsaiko ga samar da hidimomin yau da kullum ga masu amfani da su ba, bisa dogaro da cewa, mutanen sun kin bayyana bayanansu da ba su da alaka da hidimomin da suke bukata. (Fa’iza Mustapha)