logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda masu yawa yayin musayar wuta

2021-11-15 10:36:33 CRI

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda masu yawa yayin musayar wuta_fororder_d01373f082025aaf7028e8d9f6abc76d034f1a5d

Dakarun tsaron Najeriya sun kashe mayakan kungiyar masu da’awar kafa daular musulunci ta yammacin Afrika ISWAP, a musayar wutar da suka yi da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, kamar yadda rundunar sojojin kasar ta bayyana.

Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojojin Najeriya, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe wani babban jami’in soji da wasu sojojin uku a musayar wutar da suka yi a ranar Asabar a karamar hukumar Askira Uba dake jahar Borno.

A cewar Nwachukwu, a lokacin musayar wutan, sojojin sun samu taimakon jiragen yaki na sojojin sama, inda suka kashe mayakan da dama tare da lalata motocin dake daukar manyan bindigogi guda tara da sauran kayayyakin yaki na mayakan.

A sanarwar ta’aziyyar mutuwar babban jami’in sojan da sauran sojojin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana mutuwar sojojin a matsayin babbar hasara ga kasar.

Shugaba Buhari yace, Najeriya tayi rashin jaruman sojoji. Yace ya jinjina musu, tare da yin addu’ar neman rahama ga sojojin.(Ahmad)