logo

HAUSA

An bude hada hadar hannayen jari a sabuwar kasuwar BSE

2021-11-15 13:56:12 CRI

An bude hada hadar hannayen jari a sabuwar kasuwar BSE_fororder_8326cffc1e178a8290ca89c55f3d1e84a877e8ad

A yau Litinin ne aka bude hada hadar hannayen jari, a sabuwar kasuwar hannayen jari ta birnin Beijing ko BSE a takaice, inda a karon farko rukunin kamfanoni 81 suka gudanar da cinikayya a kasuwar.

An kaddamar da BSE ne watanni 2 kacal, bayan da gwamnatin Sin ta ayyana shirin kafa sabuwar kasuwar, a wani mataki da ya yi matukar samun karbuwa tsakanin masu ruwa da tsaki, wanda kuma ke da nufin magance kalubalen da kanana da matsakaitan kamfanoni ke fuskanta.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin kaddamar da kasuwar ta BSE, shugaban hukumar dake sanya ido kan harkokin cinikayyar hannayen jari ta kasar Sin Yi Huiman, ya jinjinawa matakin, yana mai bayyana BSE a matsayin muhimmin ci gaba a fannin bunkasa sauye sauye, da fadada kasuwar hannayen jarin kasar Sin.

Yi Huiman ya kara da cewa, "Matakin na da muhimmancin gaske ta fuskar bunkasa kasuwannin hannayen jari, da inganta tallafin da kanana da matsakaitan masana’antu ke samu, tare kuma da ingiza ci gaba mai kunshe da kirkire kirkire, da gyare-gyaren da ake fatan samarwa bangaren tattalin arzikin kasar”.  (Saminu)