logo

HAUSA

Sin na fatan taron shugabannin Sin da Amurka zai cimma sakamakon da zai amfani kasashen biyu da ma duniya baki daya

2021-11-15 19:06:26 CRI

Sin na fatan taron shugabannin Sin da Amurka zai cimma sakamakon da zai amfani kasashen biyu da ma duniya baki daya_fororder_中美-2

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa game da taron da shugabannin kasashen Sin da Amurka za su yi a taron manema labaran da aka saba shiryawa Litinin din cewa, wannan taron wani babban lamari ne a dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da ma huldar kasa da kasa. Jama'ar Sin da Amurka da sauran kasashen duniya, na fatan taron zai cimma sakamako mai amfani ga kasashen biyu da ma duniya baki daya.

Kamar yadda aka cimma matsaya tsakanin Sin da Amurka, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo a safiyar gobe Talata 16 ga watan Nuwamba, agogon Beijing na kasar Sin. (Ibrahim)