logo

HAUSA

Mutane 5 sun mutu a zanga-zangar Sudan

2021-11-14 17:11:58 CMG

Mutane 5 sun mutu a zanga-zangar Sudan_fororder_1114-Sudan-Ahmad

A kalla mutane biyar ne aka kashe a ranar Asabar yayin gagarumar zanga-zangar da aka gudanar a Khartoum babban birnin kasar Sudan, da sauran biranen kasar, ma’aikatar lafiyar gwamnatin kasar da aka rusa ce ta bayyana hakan.

Birnin Khartoum da sauran biranin kasar sun wayi gari da mummunan bore inda mutane ke yin zanga-zangar nuna adawa da matakin da kwamandan sojojin kasar ya dauka na baya bayan nan, wadanda suka hada da rusa gwamnatin rikon kwaryar kasar, tare da ayyana sabuwar majalisar mulki a kasar.

Masu zanga-zangar sun yi gangami a biranen Khartoum, da Bahri da Omdurman.

To sai dai, masu zanga-zangar basu samu damar kaiwa tsakiyar birnin Khartoum ba, wanda ke dauke da muhimman gine ginen gwamnati kamar helkwatar mulkin kasar, da tsohuwar fadar mulkin kasar da kuma hukumar sojoji ta kasar, sakamakon rufe babbar gadar da ta hada birane uku na kasar da kuma tarin jami’an tsaron da aka jibge a manyan titunan babban birnin kasar.(Ahmad)

Ahmad