logo

HAUSA

Yadda Sin ta yi nasarar zamanantar da kasa mai salo irin nata

2021-11-14 16:18:53 CRI

Yadda Sin ta yi nasarar zamanantar da kasa mai salo irin nata_fororder_sin

Kafin wata guda daya da ya gabata, a yayin dandalin taron tattaunawa kan ilmomin kasar Sin na kasa da kasa karo na 9 da aka shirya, tsohon shugaban kasar Serbia Boris Tadic, ya bayyana cewa, kalubalen da kasashen yamma suke fuskanta a karni na 21 ya nuna cewa, ba lallai ba ne a iya cimma burin zamanantar da kasa a bisa salo irin na kasashen yamma, yanzu haka kasar Sin ta koyar da daukacin kasashen duniya abubuwan da suka shafi zamani ta hanyar zamanantar da kasa mai salo irin nata.

Game da yadda kasar Sin ta yi nasara a tsarin zamanantar da kasa mai salo irin nata, wato ba tare da yin mulkin mallaka, da tayar yake-yake, da haddasa sabani ba, ire-iren sakamakon da hanyar kasar Sin ke kawowa duniya, abubuwa ne da suka fi jawo hankalin kwararrun kasa da kasa, musamman ma bayan da aka fitar da rahoton cikakken taro na 6 na kwamitin tsakiya karo na 19 na JKS a kwanakin baya, hanyar zamanantar da kasa mai salon kasar Sin ya kara jawo hankalin al’ummun kasa da kasa, har ma suna yin la’akari da kuma tattaunawa kan batun.

Daga tarihin ci gaban bil Adama, an lura cewa, duk da cewa kasashen yamma sun fi samun bunkasuwa a bangaren zamani, amma sun samu ci gaban zamani ne tare da haifar da wasu tsaiko, kamar ratar dake tsakanin masu arziki da matalauta, da haifar da baraka a yanayin zamantakewar al’umma, a don haka ana ganin cewa, hanyar zamanintar da kasa mai salon kasashen yamma ba shi ne mafi dacewa da sauran kasashen duniya ba.(Jamila)