logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindigar kungiyar masu tsattsauran ra’ayi da dama

2021-11-14 20:02:31 CRI

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindigar kungiyar masu tsattsauran ra’ayi da dama_fororder_buhari

A ranar 13 ga watan Nuwamba, rundunar sojojin Najeriya ta bayar da sanarwar cewa, ta yi arangama da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta ISWAP a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, inda ta hallaka ‘yan bindigar masu yawan gaske, sai dai rundunar sojojin ta yi rashin soja guda mai mukamin birgediya janar da kuma karin wasu sojojin 3, inda suka rasa rayukansu a bakin daga. A daren da lamarin ya faru, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya fidda sanarwar nuna juyayin mutuwar sojojin.(Ahmad)