logo

HAUSA

Kudaden da biya ta intanet yayin ranar gwagware ta kasar Sin ya kai Yuan triliyan 22.3

2021-11-13 16:11:05 CRI

Kudaden da biya ta intanet yayin ranar gwagware ta kasar Sin ya kai Yuan triliyan 22.3_fororder_双十一

Alkaluma daga babban bankin kasar Sin sun nuna cewa, hanyoyin biyan kudi ta intanet na kasar Sin na NetsUnion da na katin UnionPay, sun bada rahoton cewa, an biya kudade ta intanet da darajarsu ta kai yuan 22.32, kimanin dala triliyan 3.48, yayin bikin ranar gwagware ta kasar Sin ta bana, da aka fara daga ranar 1 zuwa 11 ga watan Nuwamba.

A cewar bankin, hidimomin biyan kudi na cike da nagarta da aminci, kuma yawan harkokin kasuwanci masu alaka da shi da yanayin sayayyar jama’a, ya karu sosai a lokacin, inda ake samun garabasar kayayyaki.

Kamfanin Alibaba ne ya fara bayar da garabasa a ranar gwagware ta 11 ga watan Nuwamba, a shekarar 2009, kuma tun daga sannan, ya zama katafaren lokacin sayayyar kayayyaki ta kafar intanet a duniya. (Fa’iza Mustapha)