logo

HAUSA

Riga kafin COVID-19 na kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa samun adadi mai yawa na mutanen da suka karbi allurar

2021-11-12 10:17:29 CRI

Wani rahoton bincike na Birtaniya, ya ce rigakafin kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa samun adadi mai yawa na wadanda suka karbi allurar, a wasu wurare ma, adadin ya zarce na kasashe masu arziki.

Riga kafin COVID-19 na kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa samun adadi mai yawa na mutanen da suka karbi allurar_fororder_1112-Faiza1-hoto1

Rahoton ya ce a wasu kasashe masu tasowa kamar Chile da Cambodia, galibin al’ummarsu sun karbi allurar rigakafin, yana mai alakanta nasarar da taimakon kasar Sin.

Bayanai sun nuna cewa, yanzu Chile na daga cikin wadanda ke da al’umma mafi yawa da suka karbi riga kafin a duniya, inda adadin ya kai kaso 79, kuma daya daga cikin dalilan shi ne, Chile ta saye riga kafin Sinovac mai yawa daga kasar Sin.

Riga kafin COVID-19 na kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa samun adadi mai yawa na mutanen da suka karbi allurar_fororder_1112-Faiza1-hoto2

Marubuciyar rahoton, Agathe Demarais, ta ce har ila yau, bayanan sun nuna cewa, zuwa watan Oktoba, kaso 80 na mazauna Cambodia sun karbi riga kafin, kuma wannan na nuna cewa kasashe masu tasowa sun samu nasara wajen yi wa al’ummarsu riga kafi da taimakon kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)