logo

HAUSA

Iran ta bukaci hadin gwiwar shiyyoyi don tinkarar matsalar tsaro

2021-11-12 11:23:44 CRI

Iran ta bukaci hadin gwiwar shiyyoyi don tinkarar matsalar tsaro_fororder_1112-Ahmad3-Iran-Rasha2

Sakataren majalisar tsaro ta Iran, Ali Shamkhani, ya bayyana cewa, hanya mafi dacewa ta kawo karshen matsalolin tsaro na shiyyar shi ne bullo da matakai mafi dacewa da shiyyar ta hanyar halartar dukkannin kasashen dake shiyyar.

Shamkhani ya bayyana matsalar ta’addanci, da kutsen sojojin kasashen waje, da kuma batun ’yan ci rani a matsayin manyan batutuwan dake shafar tsaron shiyyar, kamar yadda tashar talabijin din kasar ta bada rahoto.

Ya bayyana a yayin ganawa da takwaransa, Nikolai Patrushev na kasar Rasha, a yayin taron tattauna al’amurran tsaron shiyyar game da batun Afghanistan, wanda aka gudanar a Indiya, inda ya bayyana cewa, mafita game da wannan batu shi ne a yi kokarin kawo karshen daukin da wasu kasashen ke ikirarin kaiwa ta hanyar tsallaka kan iyakokin shiyyar, musamman kasar Amurka.

Haka zalika ya bukaci hadin gwiwa tsakanin Iran da Rasha, da kuma fadada kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, musamman a fannin tabbatar da tsaro da yaki da ta’addanci. (Ahmad Fagam)