logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi a taron jagororin tattalin arziki na kungiyar APEC karo na 28

2021-11-12 21:21:02 CRI

Xi jinping ya gabatar da jawabi a taron jagororin tattalin arziki na kungiyar APEC karo na 28_fororder_apec

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron kolin kungiyar APEC karo na 28 ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, inda ya gabatar da jawabi.

A cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya yi kira da a aiwatar da kudurorin APEC na putrajaya na shekarar 2040, da gina al’ummar bai daya ta al’ummun Asiya da Pacific mai makomar bai daya, a bude, mai hade dukkanin sassa, da ci gaban kirkire-kirkire, da hade dukkanin fannoni, da yin hadin gwiwar cin moriyar juna, da bunkasa hade tattalin arzikin shiyyar, da gina sahihin tsarin samar da yankin cinikayya maras shinge na Asiya da Facific cikin gaggawa.

Shugaba Xi ya ce, kamata ya yi a daga martabar hadin kai maimakon yin fito na fito, a dinke maimakon rarrabuwa, da dunkulewa maimakon bin hanyoyi daban daban, da nacewa cudanyar dukkanin sassa karkashin lemar kungiyar WTO a matsayin jigo. Ya ce, “ya dace mu maida hankali ga samar da ci gaba mai hade da kirkire-kirkire, da gabatar da alfanun fasahohin sadarwa ga karin al’ummun shiyyar Asiya da Facific. Ya kamata mu kara adadin gudummawa a fannin hadin gwiwar raya tattalin arziki da fasahohi, don tabbatar da mambobin kasashe masu tasowa sun amfana daga gare su, tare da shigar da sabon karfi ga ayyukan bunkasa ci gaba da wadatar yankin Asiya da Facific.

Shugaban na Sin ya ce kasarsa za ta shiga wata sabuwar tafiya, ta gina kasa mai bin salon gurguzu na zamani. Kaza lika Sin za ta kara bude kofofinta ga duniya, tare da raba damammakin ci gabanta da sauran sassan duniya, da ma sauran kasashe dake yankin Asiya da Facific.  (Saminu)