logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Rwanda sun yi musayar sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashensu

2021-11-12 10:59:14 CRI

Shugabannin Sin da Rwanda sun yi musayar sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashensu_fororder_1112-Ibrahim3-Sin da Rwanda

A yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame suka yi musayar sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya jaddada cewa, yana mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninsa da kasar Rwanda, kuma yana son yin amfani da damar bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, da sabon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), don zurfafa harkokin siyasa, da amincewa da juna, da karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, ciki har da gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, da sa kaimi ga ci gaba da raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

A nasa banganre kuwa, shugaba Kagame ya bayyana a cikin sakon nasa cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya, dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu take ci gaba da zurfafa, wadda ake iya gani a tsarin falsafar mutunta juna, da hadin kai da samun moriyar juna. Yana mai cewa, kasar Rwanda za ta ci gaba da fadada tare da karfafa hadin gwiwar abokantaka a dukkan fanon tsakaninta da kasar Sin.

A dai yau din ne kuma, shi ma mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, da takwaransa na kasar Rwanda Joseph Biruta, suka yi musayar sakon taya murna cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim Yaya)