logo

HAUSA

Dakarun tsaron Najeriya sun kashe ’yan bindiga 15 a yankuna masu fama da matsalar tsaro daga ranar 29 ga watan Oktoba

2021-11-12 10:32:18 CRI

Dakarun tsaron Najeriya sun kashe ’yan bindiga 15 a yankuna masu fama da matsalar tsaro daga ranar 29 ga watan Oktoba_fororder_1112-Ahmad1-Nigeria

Sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga a kalla 15 da kuma kama wasu 48 a ayyukan sindirin da suka gudanar a sassa daban daban na kasar dake fama da rikici da suka hada da shiyyar arewa ta tsakiya da arewa maso yammacin kasar a makonni biyun da suka gabata.

Bernard Onyeuko, kakakin rundunar sojojin Najeriya ya bayyanawa taron ’yan jaridu a Abuja cewa, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su a shiyyoyin biyu a lokacin ayyukan sintirin da suka gudanar daga ranar 29 ga watan Oktoba.

A cewar Onyeuko, a cikin wa’adin ayyukan sindirin, a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya kadai, sojojin sun kaddamar da hare hare masu zafi ta jiragen sama da na kasa, inda suka kashe ’yan bindigar 13.

A shiyyar tsakiyar kasar kuwa, sojojin sun kashe ’yan bindiga biyu.

Kakakin rundunar sojojin ya bayyana cewa, dakarun tsaron kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba a kokarin da suke na yaki da masu aikata muggan laifuka a dukkan sassan kasar. (Ahmad)