logo

HAUSA

Manyan jami’an diflomasiyyar Sin da Amurka sun yi tsokaci kan hadin gwiwar yaki da sauyin yanayi

2021-11-12 11:10:19 CRI

Manyan jami’an diflomasiyyar Sin da Amurka sun yi tsokaci kan hadin gwiwar yaki da sauyin yanayi_fororder_1112-Ahmad2-sauyin yanayi

Manyan jami’an diflomasiyya na kasashen Sin da Amurka sun bayyana muhimmancin hadin gwiwa bayan da kasashen biyu suka fidda sanarwar hadin gwiwa na yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi.

Xie Zhenhua, wakilin musamman na kasar Sin a taron sauyin yanayi ya bayyanawa taron ’yan jaridu bayan sanarwar da kasashen biyu suka fitar inda ya bayyana cewa, “idan aka zo batun yaki da matsalar sauyin yanayi, hadin gwiwar Sin da Amurka shi ne abu mafi muhimmanci fiye da sabanin dake tsakaninsu, hakan ya nuna cewa batun sauyin yanayi ya kasance a matsayin wani muhimmin bangare da ya fi cancantar kasashen biyu su hada kansu”.

Da yake jawabi a taron ’yan jaridun, wakilin musamman na shugaban kasar Amurka a taron sauyin yanayi, John Kerry ya bayyana cewa, “hadin gwiwa shi ne kadai hanya mafi dacewa na cimma nasarar wannan aikin. “Ba za mu iya cimma nasarar wannan buri ba har sai dukkanmu mun yi aiki tare”.

Kasashen Sin da Amurka sun fidda sanarwar hadin gwiwa a tsakaninsu a wajen taron sauyin yanayi a Glasgow, da nufin daukar matakan aiwatar da yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi ta shekarar 2020 a wajen taron sauyin yanayi na MDD karo na 26 dake gudana wato taron (COP26). (Ahmad)