logo

HAUSA

Gwamnatin Afghanistan ta karya lagon barazanar IS ta cafke mayaka 600

2021-11-11 10:21:36 CRI

Gwamnatin Afghanistan ta karya lagon barazanar IS ta cafke mayaka 600_fororder_211111-Afghanistan-Ahmad2

Gwamnatin rikon kwaryar kasar Afghanistan ta sanar a ranar Laraba cewa, ta sassauta barazanar tsaron da kungiyar dake da’awar kafa daular musulunci ta IS ko kuma kungiyar Daesh ke yadawa, inda ta bayyana cewa, jami’an tsaron kasar sun yi nasarar kama mayaka kusan 600 dake da alaka da kungiyoyin masu dauke da makamai cikin watanni sama da uku.

Kakakin gwamnatin kasar, Zabihullah Mujahid, ya bayyanawa taron manema labarai cewa, jami’an tsaron jamhuriyar musuluncin sun yi nasarar lalata sansanoni 21 na mayakan kungiyar Daesh a larduna da dama da suka hada da Kabul, Nangarhar da Herat, sannan sun cafke mayaka kusan 600 a sama da watanni uku da suka gabata.

Sakamakon karya lagon barazanar kungiyar ta IS, Mujahid ya ce, a yanzu kungiyar ta dena samun goyon bayan al’ummar kasar Afghans kuma an ci karfin ayyukan kungiyar. (Ahmad Fagam)