logo

HAUSA

Kamaru za ta yiwa kashi 50 cikin dari na ma’aikatan gwamnati riga kafin COVID-19

2021-11-11 10:32:55 CRI

Kamaru za ta yiwa kashi 50 cikin dari na ma’aikatan gwamnati riga kafin COVID-19_fororder_211111-Cameroon-Ahmad1

Ministan lafiyar kasar Kamaru, Manaouda Malachie, yace kasarsa tana da burin yiwa kashi 50 bisa 100 na ma’aikatan gwamnatin kasar wadanda sunayensu ke cikin tsarin biyan albashi riga-kafin cutar COVID-19 a cikin wata guda, ministan ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da shirin gangamin aikin riga-kafin ga ma’aikata da ’yan fansho na kasar.

An fara aikin riga-kafin ne a Yaounde, babban birnin kasar. Inda daruruwan ma’aikatan gwamnatin suka taru cikin tsanaki domin amsar riga-kafin a cibiyoyin da gwamnati ta tanada, wasu daga cikin ma’aikatan sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua farin cikinsu sakamakon amsar riga-kafin.

Ernestine Nabu, wani ma’aikacin gwamnati da aka yiwa riga-kafin, ya shedawa Xinhua jim kadan bayan karbar riga-kafin cewa, yana matukar farin cikin karbar riga-kafin, ya ce wannan ita ce kadai hanyar da za ta ba shi kariya da kuma abokan aikinsa.

Sama da ma’aikata 250,000 daga cikin adadin ma’aikatan gwamnatin kasar 528,000 ake son yiwa riga-kafin nan da ranar 10 ga watan Disamba.

Yayin da aka samu amincewar amfani da riga-kafin hudu, kasar dake yankin tsakiyar Afrika ta yi wa mutane sama da 600,000 riga-kafin a kashin farko na alluran riga-kafin kamfanin Sinopharm na kasar Sin wanda ya isa kasar a watan Afrilu, kamar yadda Malachie ya bayyanawa taron ’yan jaridu a Yaounde, babban birnin kasar a lokacin kaddamar da aikin riga-kafin. (Ahmad Fagam)