logo

HAUSA

Guterres ya yi maraba da sanarwar Sin da Amurka kan inganta ayyukan sauyin yanayi

2021-11-11 10:39:57 CRI

Guterres ya yi maraba da sanarwar Sin da Amurka kan inganta ayyukan sauyin yanayi_fororder_211111-climate action-Yaya2

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da sanarwar hadin gwiwar da kasashen Sin da Amurka suka fitar, game da inganta matakan yaki da sauyin yanayi a taron Glasgow.

Guterres ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa, "Ina maraba da yarjejeniyar da Sin da Amurka suka fitar, don yin aiki tare ta nufin kara cimma burika bisa maudu’in #ClimateAction, a cikin wadannan gwamman shekaru,".  Yana mai cewa, idan har ana bukatar magance matsalar sauyin yanayi, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai a, kuma wannan mataki ne mai muhimmanci a kuma lokacin da ya dace.

A jiya ne dai, kasashen Sin da Amurka suka fitar da sanarwar hadin gwiwar Glasgow, kan habaka matakan yaki da sauyin yanayi a cikin shekarun 2020, a ci gaba da zama na 26 na taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD wato (COP26) a Glasgow.

Bangarorin biyu sun yi alkawarin ci gaba da yin aiki tare da dukkan sassa, don karfafa aiwatar da yarjejeniyar Paris. Sun kuma amince su kafa kungiyar aiki kan inganta matakan yaki da sauyin yanayi a shekarun 2020, don inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da kuma hanyoyin da za a bi. (Ibrahim Yaya)