logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ci gaban da ya shafi kowa ita ce sahihiyar hanyar magance rashin daidaito da kawar da rikice-rikice

2021-11-10 09:34:54 CRI

Wakilin Sin: Ci gaban da ya shafi kowa ita ce sahihiyar hanyar magance rashin daidaito da kawar da rikice-rikice_fororder_驻联合国代表-张军

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana a jiya Talata cewa, samun ci gaba da ya shafi kowa da kowa, ita ce muhimmiyar hanyar magance rashin daidaito da kawar da rikice-rikice.

Zhang ya bayyana haka ne, yayin bude taron muhawara na kwamitin sulhun MDD kan nuna wariya da rashin daidaito da kuma rikice-rikice, yana mai cewa, "Ya kamata mu inganta dangantakar kasa da kasa da ke nuna mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwar cin nasara tare. Kana ya zama wajibi a tabbatar da daidaito tsakanin kasashe manya da kanana, da aiwatar da al'adu iri-iri na gaskiya, mu kuma sadaukar da kai ga ka'idoji da dalilan da suka kai ga kafa MDD, ta yadda dukkan kasashe da al'ummomi, za su iya shiga aikin tabbatar da zaman lafiya, da ci gaba, da mutuntawa tare da tsara makomar bil'adama tare."

Wakilin na kasar Sin ya ce, dangane da haka, kwamitin sulhun ya sauke muhimman ayyuka da kuma daukar nauyin abin da kasashen duniya ke bukata. Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan mambobin majalisar, wajen yin kokarin kafa kyakkyawar makoma.(Ibrahim)