logo

HAUSA

Amurka na da tarihin matsalar aminci game da batun sauyin yanayi

2021-11-10 14:44:40 CRI

Amurka na da tarihin matsalar aminci game da batun sauyin yanayi_fororder_1110-Faiza3 推送

Mujallar New Yorker ta Amurka, ta wallafa wani sharhi a shafinta na intanet a ranar 7 ga wata, inda ta yi bayani kan gazawar Amurkar ta tabuka abun kirki game da yaki da sauyin yanayi a shekarun baya-bayan nan. Sharhin ya yi bayanin cewa, abu ne mai wuya Amurka ta cimma mizanin rage hayaki mai dumama yanayi da gwamnatin Biden ta sanya, saboda haka manufofin Amurkan suke. Ya ce duk da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, nasarori kalilan Amurka ta samu. Sharhin ya ruwaito Laurence Tubiana, jami’ar diflomasiyyar Faransa da ta taimaka wajen tsara yarjejeniayr na cewa, Amurka na da tarihin matsalar aminci game da batun sauyin yanayi. (Faeza Mustapha)