logo

HAUSA

Iran ta ci alwashin kara matakan tsaronta duk da barazanar takunkuman Amurka

2021-11-10 10:11:59 CRI

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abollahian, ya jaddada aniyar manufofin tsaron kasarsa, inda ya bayyana cewa, jamhuriyar musulunci ta Iran za ta ci gaba da kara karfin tsaronta, duk kuwa da barazanar kasar Amurka ta yunkurin kakaba mata takunkumai marasa tushe.

Amir Abdollahian, ya yi wannan tsokaci ne a yayin zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa, Jean-Yves Le Drian.

Ya ce shirin karfafa tsaron ‘yancin yankunan kasa, iko ne da ko wace kasa ke da shi a duniya.

Ministan harkokin wajen na Iran ya ce, kasarsa tana kokarin bin matakai mafiya dacewa na zahiri a tattaunawar nukiliyar kasar dake tafe, inda ya bayyana aniyar Iran din ta dawowa kan teburin cikakkiyar tattaunawar dukkan bangarori kan batun nukiliyar kasar wato (JCPOA), wanda aka shirya gudanarwar a ranar 29 ga watan Nuwamba a birnin Vienna, na kasar Austria.

Amir Abdollahian, ya kuma tabo batun sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Iran, inda ya bayyana matakin da cewa, wata alama ce dake nuna cewa Iran za ta ci gaba da nuna kin amincewa da Amurka.

A nasa bangaren, Le Drian ya jaddada aniyar kasarsa ta goyon bayan cikakkiyar yarjejeniyar dukkan bangarori ta JCPOA, inda ya bayyana cewa, Faransa za ta yi dukkan bakin kokarinta don kawo karshen takaddamar.(Ahmad)