logo

HAUSA

AU ta bukaci a shirya muhimmiyar tattaunawar lalibo hanyar magance rikicin Habasha

2021-11-10 10:55:15 CRI

AU ta bukaci a shirya muhimmiyar tattaunawar lalibo hanyar magance rikicin Habasha_fororder_1110-Ahmad2

Kungiyar tarayyar Afrika (AU), ta bukaci dukkan bangarorin dake shafar rikicin kasar Habasha dasu amince su shiga muhimmiyar tattaunawar lalibo bakin zaren warware rikicin dake cigaba da ta’azzara a shiyyar arewacin kasar.

Sanawar da majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar mai mambobin kasashen 55 ta fitar a ranar Talata bayan kammala taron majalisar a ranar Litinin, inda aka tattauna game da halin da ake ciki a kasar Habasha.

Majalisar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga dukkan kokarin da babbar tawagar wakilan kungiyar AU karkashin jagorancin Olusegun Obasanjo ke yi na neman tsakaita bude wuta da yunkurin warware rikicin kasar cikin ruwan sanyi, kana tana maraba da dukkan kokarin sauran bangarorin kasa da kasa da na shiyya wadanda zasu taimaka wajen tabbatar da cimma nasarorin da aka sanya a gaba.

Tun a sanyin safiyar ranar 4 ga watan Nuwamban shekarar 2020, gwamnatin kasar Habasha take cigaba da daukar matakan soji inda take yakar sojojin dake nuna goyon baya ga kungiyar fafutukar kwato ‘yancin yankin Tigray, (TPLF).

A karshen watan Yuni, gwamnatin ta sanar da matakin tsakaita bude wuta na bangare guda a yankin Tigray, to sai dai mayakan dake biyayya ga TPLF na gaf da kwace ikon mafi yawa daga cikin yankunan shiyyar, wanda ya hada har da babban birnin shiyyar.

Majalisar wakilan kasar Habasha, ta ayyana kungiyar TPLF a matsayin kungiyar ta’addanci. (Ahmad Fagam)