logo

HAUSA

Rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta zargi ’yan tawayen M23 da kai hare-hare sansanoninta

2021-11-09 10:05:38 CRI

Rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta zargi ’yan tawayen M23 da kai hare-hare sansanoninta_fororder_211109-Congo-Faeza1

Rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta zargi ’yan tawayen M23 da kai hare-hare yankin arewa maso gabashin kasar dake da iyaka da kasar Uganda, inda rikici ya yi kamari tun daga farkon bana, saboda kasancewar dimbin kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin.

Shugaban rundunar Celestine Mbala Munsense, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ’yan tawayen na M23, sun kai hari sansanonin soji dake Chanzu da Runyonyi na lardin Kivu ta arewa, da zummar tayar da hankali a yankunan da sauran wurare, yana mai cewa, har yanzu ana ci gaba da gwabza fada.

Ya ce rundunar ta kuduri niyyar kawo karshen dukkan ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai, yana mai cewa dole ne a dakile su baki daya.

A cewarsa, sake bullowar ’yan tawayen M23 ya zo a lokacin da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ke tattaunawa da kasashe makwabta domin daidaita huldarsu, da nufin inganta yanayin tsaro a yankin, domin samun ci gaba da zaman lafiya mai dorewa a kasashen. (Fa’iza Mustapha)