logo

HAUSA

WIPO: Sin ta shigar da karin takardun bukatar ’yancin mallaka sau 2.5 fiye da Amurka a shekarar 2020

2021-11-09 10:46:25 CRI

WIPO: Sin ta shigar da karin takardun bukatar ’yancin mallaka sau 2.5 fiye da Amurka a shekarar 2020_fororder_211109-Ibrahim3-WIPO

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ruwaito daga shafin yanar gizo na hukumar kula da ’yancin mallakar fasaha ta kasa da kasa (WIPO) cewa, ofishin ’yancin mallakar fasaha na kasar Sin, ya kasance a kan gaba a duniya a shekarar 2020, inda ya bayar da rohoton gabatar da takardun neman ’yancin mallakar fasaha miliyan 1.5, wanda ya ninka na Amurka sau 2.5, wadda ta zo ta biyu.

Sakamakon ci gaba na dogon lokaci da aka samu a kasar Sin, gami da karuwar ayyukan ’yancin mallakar fasaha ko IP a wasu kasashen Asiya, ya sa yankin na Asiya zama biyu bisa uku na dukkan aikace-aikacen da aka shigar a duniya a shekarar 2020. Wannan ya kasance babban karuwar daga kashi 51.5 da aka yi rajista a shekarar 2010.

Kasar Sin dai ta samu ci gaba cikin sauri a yawan masu ’yancin mallakar fasaha a shekarar 2020, sai Jamus da Amurka da kuma Koriya ta Kudu.

An kiyasta cewa, an gabatar da takardun neman mallakar fasaha na tamburan kasuwanci miliyan 13.4 da suka shafi nau’o’in kayayyaki da ayyukan hidima miliyan 17.2 a duk duniya a cikin 2020. (Ibrahim Yaya)