logo

HAUSA

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a samar da lokaci da sarari don gudanar da ofisoshin kayayyaki a kasar Habasha

2021-11-09 10:13:39 CRI

Wakilin kasar Sin ya yi kira da a samar da lokaci da sarari don gudanar da ofisoshin kayayyaki a kasar Habasha_fororder_211109-Habasha-Ibrahim2

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a samar da lokaci da sarari don gudanar da ofisoshi na kayayyaki a kasar Habasha.

Zhang Jun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan hanyoyin warware matsalolin Afirka, da maraba da kyawawan ofisoshi na babban wakilin kungiyar tarayyar Afirka (AU) mai kula da yankin kahon Afirka, Olusegun Obasanjo, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da kasashen yankin, da su baiwa aikinsa cikakken goyon baya.

Hakazalika, kasar Sin tana maraba da tayin manyan ofisoshi da babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi mata, tana kuma sa ran inganta hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU.

Zhang ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya, musamman kwamitin sulhun MDD, su ba da lokaci da sararin da ake bukata ga kungiyar AU da sauran su, don gudanar da kyawawan ayyukansu. Yana mai cewa, yin amfani da takunkumin kasuwanci ko yanke taimako a matsayin wata hanya ta matsa lamba ga Habasha, babu abin da zai kawo illa cikas ga sulhun siyasa kawai, kuma ba zai taimaka wa bangarorin wajen warware rikice-rikicen dake tsakaninsu da ma sake gina amincewar juna ba."

Ya ce, bukatun jin kai a Habasha suna da yawa. Kana a lokacin da ake ba da tallafin jin kai ga Habasha, akwai bukatar a mutunta diyauci da shugabancin kasar, da martaba ka'idojin MDD game da ayyukan jin kai da kuma kaucewa siyasantar da al'amuran jin kai. (Ibrahim Fagam)