logo

HAUSA

Sin da Rwanda sun yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya

2021-11-09 10:22:36 CRI

Sin da Rwanda sun yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya_fororder_211109-Ruwanda-Sin-Faeza2-hoto1

Kasashen Sin da Rwanda sun yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya, wanda ya bayyana nasarorin da suka samu da kuma bude wani sabon babi na lalubo sabbin bangarorin hadin gwiwa.

Da yake jawabi yayin bikin da aka yi jiya a Kigali, babban birnin Rwanda, ministan harkokin wajen Rwanda, Vincent Biruta, ya yabawa gwamnatin kasar Sin bisa gudunmuwarta ga ci gaban kasarsa a muhimman bangarorin da suka hada da zuba jari da ginin ababen more rayuwa da fasahar sadarwa, da hakar ma’adinai da kiwon lafiya da aikin gona da kuma tsaro.

Sin da Rwanda sun yi bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya_fororder_211109-Ruwanda-Sin-Faeza2-hoto2

A nasa bangare, jakadan kasar Sin a Rwanda, Rao Hongwei, ya ce cikin shekarun da suka gabata, kasashen biyu sun kulla aminci mai muhimmanci, wanda ya karfafa dangantakarsu yayin da ake fuskantar kowanne irin sauyi a duniya.

Ya kara da cewa, dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu na ci gaba da kara zurfi. Kuma kasar Sin na alfahari da Rwanda a matsayinta na babbar abokiyar cinikayyarta da kuma babbar mai bayar da ayyukan kwangila. Ya ce yawan cinikayya tsakanin kasashen biyu a shekarar 2020, ta kai dala miliyan 321 duk da mummunan tasirin annobar COVID-19.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin za ta hada hannu da Rwanda wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga kasashen biyu, da ma kasar Sin da nahiyar Afrika baki daya. (Fa’iza Mustapha)