logo

HAUSA

ECOWAS ta jajantawa Nijer da Saliyo bisa iftila’in da ya faru a kasashen

2021-11-08 11:19:32 CRI

ECOWAS ta jajantawa Nijer da Saliyo bisa iftila’in da ya faru a kasashen_fororder_211108-ECOWAS Niger-Ahmad2

Shugaban riko na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya mika sakon ta’aziyya a madadin kungiyar, ga dukkan mutanen da iftila’i ya rutsa dasu da iyalansu a kasashen Nijer da Saliyo, mambobin kasashen biyu sun gamu da munanan bala’oi ne a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Yayin bude taron kolin shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar  ECOWAS game da batun kasashen Guinea da Mali, Akufo-Addo ya jagoranci shugabanin dake halartar taron don yin shiru na tsawon minti guda domin nuna juyayi ga mutanen da suka mutu a iftila’in da ya faru a kasashen Nijer da Saliyo.

A kalla fararen hular Nijer 69 ne aka kashe a wani harin da ‘yan bindiga suka kaddamar a ranar Talata, yayin da mutane 108 suka mutu a Saliyo a sakamakon hadarin fashewar tankar mai da yammacin ranar Juma’a.

Akufo-Addo, wanda kuma shine shugaban kasar Ghana yace, a madadin kungiyar ECOWAS, ya mika sakon jajantawa da nuna goyon baya ga kasashen Nijer da Saliyo bisa mummunan iftila’in da ya afkawa kasashen biyu. Yace sun yi matukar nuna damuwa tare da mika ta’aziyya game da faruwar bala’un. (Ahmad)